Gwamnan Kano Abba Kabir ya sake korar wasu hadimansa guda 2 bisa aikata manyan laifuka

IMG 20250726 WA0113

Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf ta amince da korar wasu Manyan Mataimaka biyu na Musamman (SSAs) bayan gano manyan laifuka daga rahotannin kwamitocin bincike da suka gudanar da bincike kan wasu hukunce-hukunce daban-daban na rashin gaskiya a aikinsu.

Wannan na cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ya fitar ranar Asabar.

A  wani mataki na ƙarshe, Gwamnan ya amince da korar Abubakar Umar Sharada, Mai Ba da Shawara na Musamman kan Shirye-shiryen Siyasa, bayan wani Kwamiti na Bincike na Musamman ya tabbatar da shi a matsayin wanda ya jagoranci bayar da belin  Sulaiman Aminu Danwawu. Rahoton ya tabbatar da rawar da Abubakar Sharada ya taka a shirin bayar da belin ta hanyar shaida da ya bayar a gaban kwamitin.

Hakazalika, Gwamnan ya kori Tasiu Adamu Al’amin Roba, Mai Ba da Shawara na Musamman a Ofishin Majalisar Zartarwa, bayan kama shi da laifin sake nannade buhunan hatsi na tallafi a wani sito da ke Sharada a shekarar 2024.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *