Ibtila’i! Ana fargabar mutuwar mutane da dama bayan da tankar mai ta fashe a Kaduna

FB IMG 1754912517225

Ana fargabar mutane da dama sun mutu sakamakon fashewar wata tankar mai a unguwar Dan Magaji da ke Zariya, Jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:30 na safiyar Litinin, a kusa da makarantar Rochas Foundation, kan hanyar Kaduna zuwa Kano daga Kwangila zuwa Dan Magaji.

A cewar Zagazola Makama, wata jaridar dake bada rahoto kan yaki da ta’addanci, haɗarin ya haɗa da tankuna biyu da kuma motocin Golf guda biyu cike da fasinjoji.

Shaidun gani da ido sun ce haɗarin ya haddasa fashewar abubuwa guda biyar a jere, wanda ya biyo bayan mummunar gobara da ta fitar da hayaki mai yawa a sama.

“Dukkan fasinjojin cikin motocin sun mutu a wurin, sai dai wani direba da ya tsira amma yana cikin mummunan hali,” in ji wani ganau.

Rahoton ya ƙara da cewa jami’an ceto, hukumomin tsaro da ma’aikatan kashe gobara sun kebe yankin, tare da shawartar direbobi da masu tafiya a ƙafa su guji hanyar yayin da ake ci gaba da aikin ceto da kwashe gawarwaki.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *