Gwamnatin Kano da Qatar Charity sun raba babura masu kafa uku guda 40 ga matasa domin dogaro da kai

FB IMG 1754886949109

Gwamnatin Jihar Kano tare da haɗin gwiwar Qatar Charity sun raba babur mai  ƙafa uku guda 40 ga wasu matasa a faɗin jihar, a wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa dogaro da kai da inganta rayuwar jama’a.

An gudanar da bikin rabon a yau tare da halartar manyan jami’an gwamnati da wakilan Qatar Charity.

Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na jihar kuma wakilin Qatar Charity a Kano, Dakta Dahir M. Hashim, ne ya wakilci Gwamna Abba Kabir Yusuf a wurin taron.

A jawabin sa, Dakta Hashim ya jinjinawa Qatar Charity bisa haɗin gwiwar da ta daɗe tana yi da jihar, yana jaddada irin gudummawar ta a fannoni daban-daban kamar samar da ruwan sha ga al’umma, kula da marayu, rabon abinci a lokacin Ramadan, da tallafin gaggawa.

Haka kuma, ya nuna godiya ga Kwamishinan Harkokin Jin Kai da Rage Talauci, Hon. Adamu Aliyu Kibiya, da Daraktan Ƙasa na Qatar Charity, Mista Assem Abu Al Shaer, da sauran manyan baki bisa goyon bayan su.

Dakta Hashim ya tabbatar da aniyar gwamnatin jihar wajen ci gaba da tabbatar da mutunci, dogaro da kai, da samar da dama iri ɗaya ga kowa a Kano.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *