Gwamnan Kano ya mika sunayen mutane biyu majalisar dokoki domin naɗa su kwamishinoni

Abba k Yusuf

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya mika sunayen mutane biyu zuwa majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni a majalisar zartarwa ta jiha.

Wannan na kunshe ne a cikin sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Asabar.

Wadanda aka mika sunayensu sune:

1. Barista Abdulkarim Kabir Maude (SAN designate) – daga karamar hukumar Minjibir, mai shekara 40.

Ana sa ran Maude zai karɓi kambun matsayin lauya mafi kololuwa wato (SAN) a gaban kotun koli gobe litinin.

Ya kammala karatun lauya a jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, sannan ya samu digiri na biyu a fannoni biyu: International Economic Law daga Maryam Abacha American University of Niger da Business Commercial Law daga Jami’ar Bayero Kano.

Barista Maude ya shafe sama da shekaru goma yana aiki a fannoni daban-daban na lauya, ciki har da shari’a, harkokin kasuwanci, da kula da kadarori.

Shi memba ne na Kungiyar lauyoyin Najeriya wato Nigerian Bar Association da kuma Chartered Institute of Arbitrators of Nigeria.

2. Dr. Aliyu Isa Aliyu – Mai Shirin zama Farfesa a fannin lissafi, mai shekara 41.

Ya samu digiri na farko a Jami’ar Bayero Kano, Masters a Jordan University of Science and Technology, sannan ya yi Ph.D. a Firat University, Turkiyya.

Dr. Aliyu ya fara koyarwa a Jami’ar Tarayya Dutse a 2014, daga bisani ya zama Associate Professor a North West University, Kano. Ya kuma yi horo a kasashen China da Cyprus. Tun 2023, yana rike da mukamin Babban Mai Kidayar Jama’a/Kakakin Hukumar Kididdiga ta Jihar Kano.

Shi ne ɗaya daga cikin masu cin gajiyar tallafin karatun waje na Kwankwasiyya, kuma ya taba rike mukamin sakataren kudi na jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Kano ya fitar ya ce a wani bangare, Gwamna Yusuf ya amince da nadin Barista Salisu Muhammad Tahir a matsayin sabon Solicitor-General da Babban Sakatare na Ma’aikatar Shari’a ta Jiha.

Kafin nadin, Barista Tahir ya kasance Daraktan mai shigar da kara wato Public Prosecution a ma’aikatar, inda ya yi fice wajen gudanar da aikinsa.

An umarci shugaban ma’aikata da ya tabbatar da kammala dukkan matakan gudanarwa domin sabon Lauyan Gwamnatin ya fara aiki daga Litinin, 29 ga Satumba, 2025.

Gwamna Yusuf ya jaddada kudirinsa na ci gaba da zabar matasa masu kwarewa da gaskiya domin kara inganta aikin gwamnati a jihar.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *