Gwamnan Kano Ya Bukaci Shugaban Kasa Ya Sauya Kwamishinan Yansandan Kano

IMG 151140 22925 1758550322304

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bukaci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta sauya kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, bisa zarginsa da rashin kwarewa da kuma yin aiki ba bisa ƙa’ida ba.

Gwamna Abba ya bayyana haka ne a jawabinsa yayin bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha, Kofar Mata.

Ya bayyana cewa, kwamishinan ‘yan sandan ya nuna rashin kishin aiki da rashin mutunta doka, bayan matakin da ya dauka na janye jami’an tsaro daga wajen taron ranar ‘yancin kai ba tare da wani dalili mai karfi ba.

“Ina kira ga shugaban ƙasa da ya dauki mataki cikin gaggawa wajen sauya kwamishinan ‘yan sandan Kano, saboda matakan da yake ɗauka sun nuna rashin kwarewa da kuma rashin adalci,” in ji Gwamna Abba.

Gwamnan ya kara da cewa, gwamnatin jihar ba za ta yi shiru ba idan jami’an tsaro suka ci gaba da gudanar da ayyukansu ta hanyar da za ta kawo barazana ga zaman lafiya da tsaro a jihar.

For Advert Or Advice Call +2348032077835

For more information about Alfijir labarai/Alfijir news fallow here 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *