Daga Aisha Salisu Ishaq
Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano (KANSIEC), Sani Lawan Malumfashi, tare da Sakataren hukumar, Anas Muhammed Mustapha, da Ado Garba, mataimakin darakta, bisa zargin badakalar kuɗi har Naira biliyan ɗaya.
Mai shari’a James Omotosho ya umarci a tsare su a gidan gyaran hali na Kuje, Abuja, bayan sun musanta laifuka guda shida da hukumar ICPC ta tuhume su da su.
Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 28 ga Janairu domin duba buƙatar belinsu.
ICPC ta zarge su da karɓar kuɗaɗe Naira miliyan 450, Naira miliyan 310 da Naira miliyan 260 ba bisa ƙa’ida ba, tsakanin Nuwamba da Disamba 2024, wanda aka ce na haram ne.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t