NNPP ta zakulo yadda aka siyarwa da Muhyi Magaji motocin gwamnati kan ƙasa da Miliyan 1.5

FB IMG 1772648165878

A yayin da ake ce-ce-ku-ce game da kwato motocin gwamnati daga kwamishinonin da suka yi murabus a gwamnatin Abba Kabir Yusuf suka bi Sanata Kwankwaso, jam’iyyar NNPP ta bankado yadda aka siyarwa da Muhyi Magaji Rimin Gado, tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, motocin hukumar a kuɗaɗe kalilan.

Mai magana da yawun NNPP na riko na jihar Kano, Engr. Ibrahim Karaye ne ya wallafa takardar cinikayyar a shafin sa Facebook.

A cikin takardar mai dauke da kwanan watan 19/8/2025 an ga gwamnati ta siyarwa da Muhyi mota kirar Toyota Corolla ,kan Naira 425,000 kacal, inda kuma aka siyar masa da Nissan Hillux kan kuɗi N833,333.33 shi ne ya hada jimilla Naira Miliyan 1 da dubu 258,333.33.

A sakon da ya wallafa, mai magana da yawun jam’iyyar ta NNPP ya sha alwashin bankado irin badakalar da gwamnatin ke aikatawa daga yanzu.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *