Da Alama Ƙasashen Turai da dama sun fi mayar da hankali kan rikicin da ke tsakanin Rasha da Ukraine, wanda ya daɗe yana barazana ga tsaron nahiyar, maimakon rikicin da ya ɓarke tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran.
Shugaban Kungiyar SEDSAC, Kwamaret Umar Hamisu Kofar Naisa ya Bayyana haka a taron manema labarai, Masana siyasa sun ce batun Ukraine na da matuƙar muhimmanci ga Turai saboda yadda yake shafar tsaron iyakokinsu kai tsaye da kuma tattalin arziƙin yankin.
Kwamaret Kofar Naisa ya jaddada cewa a halin da ake ciki, wasu ƙasashen Turai sun nuna rashin sha’awar shiga yaƙin da Amurka ta jangwalo ƙarƙashin shugabancin Donald Trump da jamhuriyar Mùsuĺùncì ta Iran.
Shugaban Kungiyar ya bada misalin yadda gwamnatin Spain ta bayyana a fili cewa ba za ta bari a yi amfani da sansanonin sojinta domin kai hari kan Iran ba, tana mai jaddada cewa tana son a warware rikicin ta hanyar tattaunawa maimakon yaƙi.
Har ila yau, ƙungiyar tsaron ƙasashen yamma ta NATO ta bayyana cewa ba za ta shiga wannan yaƙi kai tsaye ba, duk da cewa wasu ƙasashe mambobinta na iya goyon bayan matakan Amurka ta hanyoyi daban-daban.
Wannan ya nuna cewa rikicin ya fi zama takaddama tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran, yayin da Turai ke ƙoƙarin kauce wa shiga sabon yaƙi a Gabas ta Tsakiya.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t