Kotun Tarayya Ta Hana Gwamna Aiyedatiwa Sake Tsayawa Takarar Gwamnan Ondo

IMG 20260312 WA0653

Daga Aminu Bala Madobi

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a birnin Akure, babban birnin jihar Ondo, ta hana gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa, sake tsayawa takarar gwamna a zaɓen shekarar 2028.

A hukuncin da ya yanke a ranar Alhamis, mai shari’a Toyin Bolaji Adegoke ya bayyana cewa kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 (wanda aka yi wa gyara) bai amince shugaban ƙasa, mataimakinsa, gwamna ko mataimakin gwamna su ci gaba da riƙe muƙami fiye da shekaru takwas ba.

An fara rantsar da gwamna Aiyedatiwa a ranar 27 ga Disamba, 2024, bayan rasuwar tsohon gwamnan jihar, Oluwarotimi Akeredolu, domin ya kammala wa’adin mulkinsa. Daga bisani kuma an sake rantsar da shi a ranar 24 ga Fabrairu, 2025, bayan ya lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 16 ga Nuwamba, 2024.

An shigar da ƙarar ne daga wani mamba na jam’iyyar APC a jihar Ondo mai suna Kin Egbuwalo, wanda ya kalubalanci cancantar gwamnan na sake tsayawa takara. Ta bakin lauyansa, Adeniyi Akintola (SAN), mai ƙarar ya nemi kotu ta fassara sashe na 137(3) na kundin tsarin mulkin 1999 dangane da ko gwamna Aiyedatiwa yana da damar neman wa’adi na biyu.

Wadanda aka shigar da ƙarar a kansu sun haɗa da Hukumar Zabe INEC Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, gwamna Aiyedatiwa, jam’iyyar APC, da mataimakin gwamnan jihar, Olayide Adelami.

Mai shari’a Adegoke ya ce kotu ta yi la’akari ne kawai da takardun da mai ƙara da kuma waɗanda ake ƙara na farko da na biyu suka gabatar. Ya bayyana cewa takardun da sauran waɗanda ake ƙara suka shigar an ɗauke su tamkar sun watsar da su, saboda ba su halarci zaman sauraron ƙarar ba.

Kotun ta kuma yi watsi da ƙorafin da aka gabatar cewa ƙarar ba ta da tushe, tana mai cewa ƙarar ta ƙunshi hujja mai inganci. Alkalin ya ƙara da cewa barin gwamnan ya sake tsayawa takara ya kuma yi wani wa’adi na shekaru huɗu zai saɓa da hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke a shari’ar Marwa v. Nyako, wadda ta tabbatar da cewa shugaban ƙasa ko gwamna ba zai iya wuce shekaru takwas a mulki ba.

Saboda haka, kotun ta yanke hukuncin cewa ƙarar mai ƙara tana da inganci, tare da amincewa da dukkan buƙatun da ya gabatar.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *