Sakon Barka da Sallah daga Alh Musa Jidda Dan Adalan Mubi Saraki

IMG 171618 20326 1774023599813

Alh Musa Jidda Dan Adalan Mubi Saraki ya taya al’ummar musulmi murnar kammala azumi lafiya da murnar karamar Sallah

Dan Adala ya ƙara da cewa Ina taya daukakin al’ummar musulmi murnar karamar Sallah (Eid Al-ftr), tare da fatan za’a gudanar da bukukuwan Sallah lafiya.

Ina Addu’ar Allah yasa ibadunmu da mukayi na watan Ramadan su zama karbabbu, Allah ya nuna mana wani watan na Ramadan da rai da lafiya. Allah ya zaunar da yankin mu na Arewa lafiya dama kasar Najeriya baki daya, Amin.

Dan Adala ya kara da cewar kar mu manta da abubuwan da muka koya masu kyau cikin Ramadana kamar su: tsoron Allah, biyayya ga dokokinsa, Sallah a lokacinta, kyauta, sadaqa, sada zumunta, tausayawa na kasa, girmama na gaba, tausayawa marayu da marasa galihu  da dukkan ayyyuka na kwarai. Muna addu’ar Allah ya bamu ikon dorewa da wadannan kyawawan dabi’u ameen.

Muna yiwa dukkan al’ummar musulmi barka da Sallah da  fatan za’ayi  shagulgulan Sallah lafiya Ameen ameen.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *