Alh Musa Jidda Dan Adalan Mubi Saraki ya taya al’ummar musulmi murnar kammala azumi lafiya da murnar karamar Sallah
Dan Adala ya ƙara da cewa Ina taya daukakin al’ummar musulmi murnar karamar Sallah (Eid Al-ftr), tare da fatan za’a gudanar da bukukuwan Sallah lafiya.
Ina Addu’ar Allah yasa ibadunmu da mukayi na watan Ramadan su zama karbabbu, Allah ya nuna mana wani watan na Ramadan da rai da lafiya. Allah ya zaunar da yankin mu na Arewa lafiya dama kasar Najeriya baki daya, Amin.
Dan Adala ya kara da cewar kar mu manta da abubuwan da muka koya masu kyau cikin Ramadana kamar su: tsoron Allah, biyayya ga dokokinsa, Sallah a lokacinta, kyauta, sadaqa, sada zumunta, tausayawa na kasa, girmama na gaba, tausayawa marayu da marasa galihu da dukkan ayyyuka na kwarai. Muna addu’ar Allah ya bamu ikon dorewa da wadannan kyawawan dabi’u ameen.
Muna yiwa dukkan al’ummar musulmi barka da Sallah da fatan za’ayi shagulgulan Sallah lafiya Ameen ameen.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t