Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sanar da cewa ta daina amincewa da kowanne daga cikin bangarorin jam’iyyar ADC biyu, wanda David Mark ke jagoranta da kuma na Rafiu Bala, bayan nazarin hukuncin kotun ɗaukaka kara da aka yanke a ranar 12 ga Maris, 2026.
A cikin wata sanarwa da Shugaban sashen yaɗa labarai da wayar da kai na INEC, Mohammed Kudu, ya sanya wa hannu, hukumar ta ce daga yanzu ba za ta ƙara karɓar kowanne irin wasiƙa daga kowanne bangare ba.
Haka kuma, INEC ta bayyana cewa ba za ta yi hulɗa da kowanne bangare ba, kuma ba za ta sa ido kan taruka, zaɓukan cikin gida (congresses), ko manyan tarukan jam’iyyar (conventions) na bangarorin biyu ba, har sai kotu ta yanke hukunci kan rikicin.
Bugu da ƙari, hukumar ta sanar da cewa za ta cire sunan David Mark daga kundin bayananta na yanar gizo.
Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya samo asali ne bayan Rafiu Bala, wanda a baya ya kasance mataimakin shugaban jam’iyyar ADC kafin kwamitin riko karkashin jagorancin David Mark ya karɓi ragamar jam’iyyar, ya garzaya kotu domin ƙalubalantar sahihancin shugabancin sabon kwamitin.

Daily Nigerian
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t