Nasarun Minallahi: DSS Sun Cafke Wata Matashiya Kan Yiwa ‘Yan Bindiga Safarar Harsashai A Kano

FB IMG 1775073151878

Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Najeriya (DSS) ta sanar da cafke wata matashiya mai shekaru 25, Nafisa Usman, bisa zargin safarar harsasai ga ‘yan bindiga, a wani samame da ta kai a birnin Kano.

A cewar majiyoyin tsaro, an kama wadda ake zargin ne a wani babban tashar mota yayin da take kokarin jigilar harsasai da aka boye cikin buhunan kayan abinci, domin kai su zuwa yankin Kankara da ke Jihar Katsina.

Rahotanni sun nuna cewa jami’an DSS sun samu nasarar cafke ta ne bayan samun sahihan bayanai, lamarin da ya ba su damar dakile wata hanyar safarar makamai da ake zargin tana taimaka wa ayyukan ‘yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma.

Binciken farko ya nuna cewa harsasan da aka kwato, kimanin guda 200, an kawu su ne daga Lafia, babban birnin Jihar Nasarawa, kafin a kawo su Kano domin a tura su zuwa maboyar ‘yan bindiga.

Majiyoyi sun ce wadda ake zargin ta amsa cewa ta shafe kusan watanni biyu tana wannan harka, inda ta ke karbar kayayyaki daga wani da ake kira “Teso”, wanda ake zargin yana aiki tare da wani soja a Lafia.

Haka kuma, ta ce tana kai harsasan ga wani shugaban ‘yan bindiga mai suna Mallam Haruna, tare da wasu da ake kira Buba da Abu, wadanda ke aiki a cikin dazukan yankin.

A nata bangaren, wadda ake zargin ta bayyana nadama kan shigarta cikin wannan aiki, tana mai cewa a yanzu ta shirya bayar da hadin kai ga jami’an tsaro domin taimakawa bincike.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *