Babban Hafsan Sojin ƙasa na Amurka, Randy A. George, ya yi murabus daga mukaminsa nan take bayan umarni daga Sakataren Yaƙi, Pete Hegseth.
Rahotanni sun bayyana cewa Hegseth ne ya buƙaci Janar George ya sauka daga mukaminsa, kodayake ba a bayyana cikakken dalilin da ya sa aka ɗauki matakin ba.
A wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar yaƙi, Sean Parnell, ya fitar, ya ce:
“Janar Randy George ya yi ritaya nan take daga matsayin Babban Hafsan Sojin ƙasa na Amurka. Muna godiya da irin gudunmawar da ya bayar tsawon shekaru.”
Bayan ficewarsa, mataimakin Babban Hafsan Soji, Christopher LaNeve, shi ne ya karɓi ragamar shugabanci na wucin gadi.
Kuna ga wannan ya nuna ana galaba akan Amurka ko kuwa?
A Yau News
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t