Labari Mai Dadi: Gwamna Yusuf Ya Kammala Biyan Bashin N32bn Na Garatuti Da Tallafin Iyalan Mamata

IMG 20260409 WA0614

Daga Aminu Bala Madobi

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya biya ragowar Naira biliyan 32 daga cikin bashin Naira biliyan 48 da ya gada na garatuti da kuma kudaden tallafi ga ‘yan fansho da iyalan ma’aikatan gwamnati da suka rasu.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan, Mustapha Muhammad, ya fitar a ranar Laraba, 8 ga Afrilu, 2026.

Gwamna Yusuf ya ce, “A yau Laraba, 8 ga Afrilu 2026, muna biyan karin Naira biliyan 5 a karkashin kashi na shida na biyan bashin.

Yayin kaddamar da biyan kudin, gwamnan ya ce matakin na daga cikin yunkurin gwamnatin sa na cika alƙawuran da ta ɗauka, tare da tabbatar da jin daɗin tsoffin ma’aikata bayan sun gama yiwa jihar hidima a lokacin da suke ganiyarsu

Gwamna Yusuf ya ce gwamnatin sa ta gaji bashin kudaden ‘yan fansho da yawan su ya kai naira biliyan 48, sai dai yanzu haka ta biya kimanin naira biliyan 32, wanda kuma wannan shi ne karo na 6 da gwamnatin sa ta biya kudin.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma sha alwashin ci gaba da biyan sauran bashin ‘yan fanshon a matakai daban-daban domin rage wahalhalun da masu ritaya ke fuskanta.

Ya kara da cewa, “Na yi farin cikin sanar da cewa gwamnatin jihar ta riga ta biya Naira biliyan 27 a kashi biyar zuwa karshen watan Disambar 2025 daga cikin bashin da muka gada.”

Gwamnan ya sake bai wa ma’aikatan gwamnati tabbacin cewa matsalar jinkirin biyan garatuti da kudaden tallafin mutuwa za ta zama tarihi kafin karshen zangon mulkinsa na farko.
Haka kuma, ya yabawa shugabanni da mambobin Kungiyar ‘Yan Fansho ta Kasa (NUP) da Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) bisa fahimta da hadin kai da suka nuna.

Ya gode musu bisa goyon bayan da suka bai wa kokarin gwamnatin jihar wajen kawo sauki mai dorewa ga ‘yan fansho da iyalan mamatan ma’aikata.

Yayin da yake taya wadanda suka amfana murna, gwamnan ya bukace su da su yi amfani da kudaden cikin hikima.
A nasu bangaren, Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Kano, Hajiya Bilkisu Maimota, da Shugaban Hukumar Kula da Asusun Fansho na Jihar Kano, Alhaji Habu Muhammad Fagge, sun yaba da jajircewar gwamnan wajen biyan dimbin bashin cikin shekaru uku na farkon mulkinsa.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *