Daga Rabi’u Usman
Babbar Kotun Shari’ar Musulunci dake zaman ta a Filin Hockey Karkashin jagorancin mai shari’ah Dr. Umar Sunusi Dan Baba, ta Cigaba da sauraron Karar Iyalan marigayi Alhaji Baballe Ila suka shigar gaban ta.
A zaman kotun na wannan rana, kotun ta tambayi Dan aiken kotun me suna Zayyanu shin ko ya idar da Sakon kotun Wanda akace ya kaiwa Wanda akayi kara na 1 Nasiru Baballe Ila da Wanda akayi kara na 2 Alhaji Yusuf Garba Ali?
Saidai Zayyanu ya baiwa Kotun amsa da cewar bai samu Wanda ake kara na 1 Nasiru Baballe Ila ba, sannan Wanda akayi kara na 2 Yusuf Ali bashi da lafiya amma Dan uwansa yace a kaiwa Lauyan sa me Suna Hashim Aminu Mu’az Wanda Daman shine lauyan da yake tsaya masa.
Zayyanu ya kaiwa Lauyan Yusuf Garba Ali Barr Hashim Aminu Mu’az ya karɓa kuma ya rattaba hannu a ranar 7 ga watan Aprilun da muke Ciki.
Barr Abbas Sulaiman Magashi Shine Lauyan da yake tsayawa Iyalan marigayi Alhaji Baballe Ila, ya roki kotun data bayar da Umarnin lika sammaci a kofar Gidan Nasiru Baballe Ila da aike masa ta wayar hannu da kuma inda akasan yana zama dogaro da wani sashe na kundin Shari’ah.
Daga Nan kotun ta amince da rokon Lauyan Masu kara, Kuma tayi Umarnin lika sammaci a kofar Gidan Wanda akayi kara na 1 Nasiru Baballe Ila tare da aike masa ta wayar hannu da kuma inda akasan yana zama.
Sannan kuma kotun ta yi Umarnin a aike da Notice ga Lauyan Yusuf Garba Ali Wanda ya karɓi sammaci kuma ya sanya hannu a takardar shaidar karɓa, tare da bayyana cewar kotun za ta Cigaba da shari’ar Koda basu zo kotun ba dogaro da Wani Nassi da kuma Oda 3 rule 5 2021 ABCD.
A karshe kotun ta sanya ranar 29 ga watan Aprilun shekarar da muke Ciki domin Cigaba da sauraron karar.
Tunda farko dai, Iyalan marigayi Alhaji Baballe Ila ne suka shigar da rokon a raba musu Gadon wani Gareji da Mahaifin su ya rasu ya bari, sai kuma kwatsam wani Mutum me suna Alhaji Yusuf Garba Ali ya bayyana cewar wannan Garejin Mallakin sa ne sakamakon siyan da yayi a wajen Nasiru Baballe Ila.
Jin hakan ne tasa Iyalan marigayi Alhaji Baballe Ila suka Garzaya Babbar kotun shari’ar Musulunci dake zaman ta a Filin Hockey suka shigar da kara domin tabbatar da an fitar wa da kowanne bangare hakkin sa.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t