Ƙungiyar Progressive Next Generation nitiative (PNGI) ta yaba wa Hukumar Tattara Haraji, Rarraba Kuɗi da Tsare-tsaren Kuɗi ta Ƙasa (RMAFC) ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Dr. Mohammed Bello Shehu, bisa abin da ta bayyana a matsayin manyan nasarori da aka samu cikin shekaru uku na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A cikin wata sanarwa da jigon ƙungiyar, Hon. Jeffrey Omoh Ozemegwa ya fitar, PNGI ta ce hukumar ta nuna ƙwazo da jajircewa wajen inganta samar da kuɗaɗen shiga na ƙasa, tabbatar da adalci wajen rarraba kuɗaɗen shiga, da kuma tallafa wa ‘yancin cin gashin kai na kuɗi ga ƙananan hukumomi, wanda hakan ke ƙarfafa ginshiƙin tattalin arzikin ƙasar.
Sanarwar ta bayyana cewa, ɗaya daga cikin fitattun nasarorin hukumar a wannan lokaci shi ne haɗin gwiwar da ta yi da Hukumar Haraji ta Tarayya (wadda yanzu ake kira Nigeria Revenue Service) wajen gudanar da wani shiri na dawo da kuɗaɗen shiga a faɗin ƙasa, wanda ya ƙara yawan kuɗin shiga cikin Asusun Tarayya. PNGI ta ce dawo da sama da Naira biliyan 50 tare da inganta sa ido da bin ƙa’idoji sun taimaka wajen ƙaruwar kuɗaɗen shiga na Asusun Tarayya.
Ƙungiyar ta kuma yaba da aikin tantance rijiyoyin mai da filayen iskar gas da ake taƙaddama a kai a yankin Neja Delta, tana mai bayyana hakan a matsayin babban mataki na tabbatar da adalci da sahihanci wajen tattarawa da rarraba kuɗaɗen shiga tsakanin jihohin da ke haƙo mai. Ta ce wannan mataki ya taimaka wajen warware tsofaffin matsaloli da kuma ƙara yarda da tsarin rarraba kuɗaɗen shiga.
Hon. Ozemegwa ya kuma jinjina wa hukumar kan ƙaddamar da nazari kan tsarin rarraba kuɗaɗen shiga, wanda aka daɗe ana jira. Ya bayyana cewa tsarin da ake amfani da shi tun shekarar 1992 bai taɓa samun cikakken bita ba tsawon shekaru da dama. Ya ce fara wannan aiki a shekarar 2025 wata muhimmiyar kafa ce wajen ƙarfafa tsarin tarayya da kuma daidaita rarraba kuɗaɗen shiga da halin da tattalin arziki yake ciki a yanzu.
Sanarwar ta ƙara da cewa duk da cewa har yanzu ba a kammala sabon tsarin ba, tattaunawar da ake yi da kuma amfani da bayanai na kimiyya da hukumar ke yi na nuna ƙuduri da gaskiya wajen tabbatar da daidaito da ci gaban ƙasa. PNGI ta kuma lura cewa, duk da rashin sabon tsarin, rabon kuɗaɗe ga jihohi ya ƙaru matuƙa sakamakon ƙaruwar kuɗaɗen shiga, wanda ya taimaka wa gwamnatocin jihohi wajen sauke nauye-nauyensu da gudanar da ayyuka.
Ƙungiyar ta kuma yaba da goyon bayan da hukumar ke bai wa ‘yancin cin gashin kai na kuɗi ga ƙananan hukumomi, musamman bayan hukuncin Kotun Ƙoli da ya tabbatar da hakan. Ta ce hulɗar da hukumar ke yi da Ƙungiyar Ƙananan Hukumomi ta Ƙasa (ALGON) wani babban mataki ne na tabbatar da cewa ƙananan hukumomi sun samu ƙarfi wajen kawo ci gaba a matakin ƙasa.
Hakazalika, PNGI ta yaba da ƙaddamar da sabon tsarin tattara bayanai a fannin ma’adinan ƙasa, tana mai cewa wannan mataki zai taimaka wajen ƙara kuɗaɗen shiga daga wannan fanni da kuma rage dogaro da mai. Ta jaddada cewa bunƙasa kuɗaɗen shiga daga fannoni marasa alaƙa da mai na da matuƙar muhimmanci ga daidaiton tattalin arzikin ƙasa.
Sanarwar ta kuma nuna irin rawar da hukumar ta taka wajen tallafa wa amincewa da Dokar Haraji ta Nijeriya ta 2025 da kuma sabuwar Dokar RMAFC ta 2025, inda ta bayyana su a matsayin manyan nasarori da za su ƙarfafa tsarin kuɗi na ƙasa, inganta tattara kuɗaɗen shiga da kuma ƙara ƙarfafa ikon sa ido na hukumar.
Hon. Ozemegwa ya ƙara da cewa sauye-sauyen cikin gida da hukumar ta aiwatar, ciki har da horas da ma’aikata, amfani da tsarin zamani wajen auna aiki, da shirye-shiryen gina ƙwarewar ma’aikata, sun taimaka wajen sake fasalta hukumar domin inganta aiki da samar da ingantaccen aiki.
Ya ce: “Ƙungiyar Progressive Next Generation Initiative ta fahimci muhimmiyar rawar da RMAFC ke takawa a tsarin tattalin arzikin Nijeriya. Abin da muka gani cikin shekaru uku da suka gabata ƙarƙashin jagorancin Dr. Mohammed Bello Shehu shi ne cikakken misali na jajircewa wajen kula da kuɗi yadda ya kamata, ƙarin kuɗaɗen shiga, tabbatar da adalci wajen rarraba su, da kuma gyara tsarin hukumar. Waɗannan ƙoƙari na ƙarfafa Asusun Tarayya tare da tallafa wa daidaiton tattalin arziki a ƙasa baki ɗaya.”
Ya ƙara da cewa: “Muna yaba wa hukumar musamman kan ɗaukar wannan muhimmin mataki na fara bitar tsarin rarraba kuɗaɗen shiga bayan fiye da shekaru talatin. Wannan mataki ne mai ƙarfin hali da muhimmanci domin tabbatar da cewa rarraba kuɗaɗen shiga a Nijeriya ya dace da yanayin yau da kuma nauyin da kowace gwamnati ke ɗauka.”
Ƙungiyar ta kuma yaba da haɗin gwiwar da hukumar ke yi da manyan cibiyoyi kamar Hukumar Haraji ta Nijeriya, Babban Bankin Nijeriya (CBN) da sauran masu ruwa da tsaki, tana mai cewa haɗin gwiwa tsakanin hukumomi na da matuƙar muhimmanci wajen inganta tattara kuɗaɗen shiga, sa ido da kuma rarrabawa.
Don haka PNGI ta yi kira ga duk masu ruwa da tsaki, ciki har da hukumomin gwamnati, kamfanoni masu zaman kansu da ƙungiyoyin farar hula, da su mara wa sauye-sauyen harkokin kuɗi da RMAFC ke jagoranta baya, tana mai jaddada cewa ɗorewar ci gaban ƙasa na dogara ne da ingantaccen tsarin tattara kuɗaɗen shiga da kuma sarrafa su yadda ya dace.
Sanarwar ta ƙare da sake jaddada goyon bayan PNGI ga duk wani gyara da zai ƙarfafa tsarin kuɗi na ƙasa da kuma tabbatar da cewa ana sarrafa kuɗaɗen jama’a ta hanyar da za ta kawo ci gaba, daidaito da walwala ga duk ‘yan Nijeriya.
“A madadin Ƙungiyar Progressive Next Generation nitiative, ina yaba wa Shugaban RMAFC, Dr. Mohammed Bello Shehu, tare da ɗaukacin shugabanni da ma’aikatan hukumar bisa ƙwazo, ƙwarewa da sadaukarwa ga hidimar ƙasa. Muna ƙarfafa su da su ci gaba da wannan tafiya ta gyara da ƙirƙire-ƙirƙire domin amfanin ƙasa baki ɗaya,” inji sanarwar.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t