An Dakatar Da Wasu Alkalai Da Ma’aikata Bayan Samunsu Da Wasu Laifuka A Kano

FB IMG 1766328120482

Hukumar Kula da Harkokin Shari’a ta Kano ta ɗauki matakan ladabtarwa kan wasu alkalan kotuna da ma’aikata bayan samunsu da laifukan cin hanci, nuna son kai da karya dokokin aiki.

Matakin ya biyo bayan taron hukumar karo na 89 da aka gudanar ranar 16 ga Afrilu, 2026, inda aka amince da rahoton binciken kwamitin karɓar ƙorafe-ƙorafe (JPCC).

A cikin matakan da aka ɗauka, an dakatar da wasu alkalai daga gudanar da shari’a, an rage wa wasu ma’aikata matsayi, yayin da aka bai wa wasu gargaɗi mai tsanani.

Mai magana da yawun kotunan jihar, Baba Jibo Ibrahim, ya ce an ladabtar da Salisu Buhari Mandawari na Kotun Shari’a ta Rogo, inda aka rage masa matsayi tare da dakatar da shi na tsawon shekaru uku kan zargin karɓar cin hanci.

Haka kuma, an dakatar da Umar Sunusi Danbaba na tsawon shekaru uku bisa zargin nuna son kai da rashin kula da kuɗaɗe.

Bugu da ƙari, an hukunta wasu ma’aikatan kotu da suka haɗa da magatakarda bisa zargin karɓar cin hanci, yayin da aka cire wani jami’i daga mukaminsa saboda bayar da rasiti mai saɓani.

Hukumar ta jaddada aniyarta na tabbatar da gaskiya da riƙon amana a harkokin shari’a, tana mai gargadin cewa ba za ta lamunci duk wani nau’i na rashin ɗa’a ba.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *