Daga Rabiu Usman
Babbar kotun tarayya me lamba 1 dake zaman ta a kano Karkashin me Shari’ah ML Shu’aibu ta Cigaba da sauraron karar da wani Mawaki me Suna Isa Ibrahim Zage ya shigar gabanta.
Inda yake zargin Dan Uwansa Mawaki Dauda Adamu Kahutu Rarara da satar masa Fasaha bayan ya saki wakar sa me Suna Jirgin Ceto a ranar 12 ga watan Disambar shekarar 2022, yayin da shi kuma Dauda Adamu Kahutu Rarara ya saki tasa a ranar 25 ga watan Fabarairun shekarar 2023.
A zaman kotun na wannan rana, an rufe sauraron shaidun masu kara, inda za’a fara sauraron shaidun Wanda akayi kara a zaman kotun na gaba yayin da ake sa ran Wanda akayi kara Dauda Adamu Kahutu Rarara zai bayyana a gaban kotun domin amsa wasu tambayoyi.
Bayan fitowa daga kotun ne muka zanta da Lauyan Wanda akayi kara Rarara wato Barr Abdulmunafi Ibrahim Ma’aji, Inda yayi mana karin Haske dangane da zaman da ya wakana *….. INSERT…..*
A nasa bangaren Lauyan me kara Isa Ibrahim Zage, wato Barr Muhammad Sulaiman Ahmad Wanda akafi sani Nazeer, shima ya magantu dangane da zaman kotun da ya gudana *….. INSERT…..*
A karshe kotun ta sanya ranar 18 ga watan Yunin shekarar da muke Ciki domin Cigaba da sauraron karar.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t