Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin dawo da Biliyan 1.8 da aka cire daga albashin ma’aikatan jihar

FB IMG 1775317212372

Gwamnatin Jihar Kano ta kafa wani kwamitin mutum 12 domin dawo da naira biliyan 1.8 da aka ce an cire ba bisa ƙa’ida ba daga albashin ma’aikatan gwamnati ta hannun kamfanonin bada lamuni masu zaman kansu.

Haka kuma gwamnatin ta dakatar da duk wata sabuwar yarjejeniyar rance tsakanin ma’aikatan gwamnati da kamfanonin lamunin, tana mai cewa daga yanzu ba za ta ƙara shiga tsakani a irin waɗannan yarjejeniyoyi ba.

Sakataren Gwamnatin Jiha, Umar Faruq Ibrahim, ya bayyana cewa wani bincike mai zaman kansa ya gano yadda wasu kamfanonin bada lamuni ke cire kuɗi daga albashin ma’aikata fiye da yadda doka ta tanada.

A cewarsa, dokar ta amince ne kada a cire fiye da kaso ɗaya bisa uku na albashin ma’aikaci, amma binciken ya nuna an karya wannan ƙa’ida.

Ya ce Majalisar Zartarwar Jihar ta amince da rahoton binciken tare da bai wa kwamitin da Kwamishinan Kuɗi, Ismaila Aliyu Danmaraya, ke jagoranta umarnin gano duk ma’aikatan da lamarin ya shafa, ko suna raye ko sun rasu, domin mayar musu da kuɗaɗensu.

SSG ɗin ya kuma bayyana cewa binciken ya wanke tsohon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Abdullahi Musa, daga zargin hannu a badakalar.

Ya ƙara da cewa tun farko an yi kuskuren bayyana cewa kuɗin da suka ɓace sun kai naira biliyan 1.5, sai dai binciken ya tabbatar da cewa adadin ya kai naira biliyan 1.8.

Gwamnatin ta kuma nuna damuwa kan yadda ma’aikata ke ci gaba da karɓar lamuni daga kamfanoni masu zaman kansu, inda ta bayyana cewa jimillar bashin da ake bin ma’aikatan gwamnati a yanzu ya kai kusan naira biliyan 13.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *