Alh Murtala Sule Garo Ya Taya Al’ummar Musulmi Murnar ƙaramar Sallah

IMG 20250330 084334

Tsohon dan takarar mataimakin gwamnan jihar Kano a jam’iyyar APC, Alhaji Murtala Sule Garo, ya taya daukacin al’ummar Musulmi murnar bikin Karamar Sallah.

A cikin sakonsa na taya murna, Garo ya yi kira ga Musulmi da su ci gaba da rayuwa bisa darussan da suka koya a watan Ramadan, kamar hakuri, yafiya, jin kai da taimakon juna.

Ya kuma jaddada cewa azumin watan Ramadan lokaci ne da ke ƙarfafa dangantaka tsakanin bawa da Mahaliccinsa. A cewarsa, darussan da ke cikin watan Ramadan dole ne su ci gaba da wanzuwa a cikin al’umma domin samar da zaman lafiya da ci gaban kasa.

Garo ya bukaci al’ummar Musulmi, musamman na jihar Kano, da su yi addu’o’i domin zaman lafiya da yalwar arziki. Ya kuma yi fatan Allah ya karɓi ibadun da aka gudanar a cikin watan Ramadan, ya ba kowa lafiya, da zaman lafiya, da kuma bunkasar tattalin arziki.

“Allah ya karɓi ibadunmu, ya ba mu lafiya da zaman lafiya. Amin,” in ji Murtala Sule Garo.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *