Allah Ya Yiwa Wani Alhaji Rasuwa Daga Jihar Kano A Garin Makkah

Wani Alhaji daga Jihar Kano ya rasu a Makkah a Hajjin bana 2022

Alfijr ta rawaito hukumar Kula da Jin Daɗin Alhazai ta Jihar jihar Kano ta sanar da rasuwar ɗaya daga cikin alhazanta na Hajjin bana, mai suna Sani Idris Mohammed a garin Makkah.

Alfijr Labarai

Babban Sakataren hukumar jin dadin alhazan ne, Abba Muhammad Dambatta ya aike wa manema labarai da sanarwar,

Hukumar alhazan ta ce marigayin ya fito ne da ga Ƙaramar Hukumar Madobi.

Marigayin ya rasu ne a ranar Juma’a, da ta gabata, sai dai kuma shugaban bai faɗi dalilin rasuwar Alhajin ba.

Alfijr Labarai

Babban Sakataren ya ƙara da cewa tuni a ka yi jana’izar mamacin a Masallacin Harami na Makkah, sannan a ka binne shi a makabartar Shira.

Slide Up
x