An ɗage taron mahaddata Qur’ani da za a yi a Abuja

IMG 20250215 104602

Tun farko dai an saka ranar Asabar 22 ga watan Fabrairu na 2025 a matsayin ranar da za a gudanar da taron

Rahotanni sun nuna cewa an ɗage taron mahaddata al-Qur’ani da ake yi wa laƙabi da Qur’anic Convention a Turance da ya rage ƙasa da mako biyu wanda za a gudanar a Abuja kamar yadda BBC Hausa ta bayyana.

An dai ranar Asabar 22 ga watan Fabrairu na 2025 a matsayin ranar da za a gudanar da taron da ake sa ran zai samu mahalarta waɗanda mahaddata Qur’ani ne sama da dubu 60 daga ciki da wajen Najeriya.

Wani ɗan kwamitin tsara taron wanda bai so a ambaci sunansa ba ya shaida wa BBC cewa, “tun daren jiya Alhamis aka ɗage yin wannan taro.

Sai dai kuma majiyar ba ta tabbatar wa da BBC dalilin da ya sa aka ɗage taron ba da kuma yaushe ne sabon lokacin da za a yi taron a nan gaba.

Majalisar Koli Kan Sha’anin Addinin Musulunci a  Najeriya NSCIA, wacce Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Abubakar Sa’ad na III ke jagoranta ta bayyana cewa an ɗage yin babban taron Alƙur’ani na ƙasa da aka shirya saboda yawan mutanen da suke sha’awar zuwa.

A cikin wata sanarwa da Majalisar ta fitar ta bayyana cewa al’umma daga ko’ina a fadin Najeriya da ma sauran ƙasashen ƙetare sama da 500,000 ne suka nuna sha’awar zuwa wannan gagarumin taron inda ita kuma majalisar ta tsara samar da wurin mutum 60,000 ne kacal.

Wannan ya sa majalisar ta ga ya zama dole ta sake shiri wanda kuma take sa ran bayyana sabuwar ranar da za a gudanar da taron bayan kammala azumin wannan shekara.

Aminiya

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *