An daure tsohon limamin Makkah Sheikh Saleh al-Taleb shekaru 10 a gidan yari

Alfijr ta rawaito mahukuntan kasar Saudiyya sun yanke wa Sheikh Saleh al-Taleb, tsohon limamin masallacin Makkah mafi tsarki na Musulunci hukuncin daurin shekaru goma a gidan yari.

Alfijr Labarai

A cewar kungiyar kare hakkin ‘Frisoners of Conscience’. Kotun daukaka kara ta soke hukuncin farko da kotun hukunta manyan laifuka ta musamman ta yanke na wanke Sheikh Al-Taleb, a maimakon haka ta yanke masa hukuncin dauri a hukumance a cewar kungiyar kare hakkin bil adama.

Tun da farko dai an kama Sheikh Saleh al-Taleb ne a watan Agustan 2018.

Babu wani bayani a hukumance kan tsare matashin mai shekaru 48, amma kungiyoyin kare hakkin sun ce an kama shi ne bayan da ya gabatar da huduba kan aikin musulmi na tofa albarkacin bakinsa a bainar jama’a. .

Alfijr Labarai

Ga waccan wa’azin da ka iya zama dalilin kama shi:

Saudiyya ta shahara wajen daure masu fafutuka, da ‘yan jarida, da masu wa’azi akai-akai ba tare da wani dalili ba.

Rahotanni sun ce an kama wasu masu wa’azi da dama tun a shekarar 2017, ciki har da wasu da suka yi kira da a sasanta tsakanin kasashen yankin Gulf a lokacin da Saudiyya ta kitsa kai farmaki kan makwabciyarta Qatar

. Yawancin wadancan limaman har yanzu suna gidan yari, duk da dangantakar da ke tsakanin makwabta tun lokacin da aka daidaita.

Alfijr Labarai

A makon da ya gabata ne mahukuntan Saudiyya suka yanke wa Salma Al-Shehab dalibar da ke karatun digiri na uku hukuncin daurin shekaru 34 a gidan yari saboda ta wallafa a shafinta na Twitter tana sukar gwamnati, lamarin da ya janyo cece-kuce a duniya.

Kamar yadda jaridar The kashmir monitor ta wallafa

Slide Up
x