Tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa, Hajiya A’isha Muhammadu Buhari, ta bayyana wani lamari mai tayar da kura, inda ta ce wani babban malamin addinin Musulunci na bibiyarta tare da neman kusanci da ita ba tare da yardarta ba.
A’isha Buhari ta bayyana hakan ne a cikin wani saƙo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, inda ta nuna ɓacin ranta da gargaɗi mai tsanani ga malamin, tana mai cewa idan har bai daina bibiyarta da nemanta ba, za ta fito fili ta tona masa asirin da ya ɓoye.
Ta ce tana mamakin yadda mutumin da ake kallonsa a matsayin abin koyi da jagora a addini zai rika aikata irin wannan ɗabi’a, alhali ana tsammanin ya kasance yana koyar da tarbiyya da tsoron Allah.
“Na yi shiru na dade, amma idan har bai daina wannan bibiyar ba, zan fito na faɗi duk abin da na sani a kansa,” in ji A’isha Buhari.
DCL Hausa
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t