Annoba! Fadan Daba yayi sanadin mutuwar Mutane 2 kofar mata Kano

B9

Rundunar yan Sandan jahar Kano, ta tabbatar da Rasuwar mutane 2, biyo bayan fadan Daba da ake zargin wasu matasa daga unguwannin , Zango da kuma Kofar Mata.

Alfijir labarai ta rawaito Kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya tabbatar da hakan a zantawarsa da manema labarai a yau Litinin.

Kiyawa, ya ce tun a ranar Lahadi, suka samu kiraye-kiraye daga unguwar Kofar Mata , daidai lokacin da aka tashi wasa a filin wasa na Sani Abacha Stadium, Inda wasu matasa suka dinga yin fadace-fadacen daba Tsakanin Unguwannin.

Kiyawa ya kara da cewa bayan Samun rahotannin marasa Dadi kwamishinan yan Sandan jahar Kano, CP Salman Dogo Garba, ya Tura dakarun Yan Sanda da gaggawa wajen da lamarin ya Faru, kuma sun Samun rahotan Mutuwar mutane 2.

Rundunar ta ce yanzu haka an dukufa wajen gudanar da bincike don ganin duk wanda yake da hannu akan fadace-fadacen dabar, ya zo don ya fuskanci hukunci.

A karshe rundunar ta ja hankalin al’umma, musamman wajen taimaka wa jami’an Yan Sandan da bayanan sirri, tunda dai wadanda suke aikata laifukan Yan unguwane.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *