Asibitin Mal Aminu Kano Zai Fara Dashen Ɓargo

Alfijr ta rawaito Asibitin koyarwa na Mal Aminu Kano, AKTH, a ranar Litinin ya ƙaddamar da wani sabon sashin kula da cututtukan jini, wanda suka tabbatar da za a fara dashen ɓargo a cibiyar, inda asibitin zai kasance asibitin koyarwa na biyu a Nijeriya da zai riƙa yin dashen ɓargo a kasar.

Alfijr Labarai

Farfesa Abba Sheshe wanda shine shugaban asibitin, ya bayyana haka a wurin kaddamar da cibiyar a hukumance, wanda wani Injiniya Umar lbrahim ya bada ita a matsayin gudunmawa ga AKTH

Ya bayyana cewa asibitin koyarwa na jami’ar jihar Lagos ne ya fara samun nasarar dashen ɓargo a Najeriya.

Ya kuma jaddada cewa kayan aikin da za a sanya a cibiyar za su taimaka a samu nasarar dashen ɓargo a asibitin.

Alfijr Labarai

Shehe ya yabawa lbrahim wanda yayi wannan jin kai ga asibitin, kuma yayi addu’ar Allah ya saka masa da alkhairi.

A nasa banga madadin wanda ya bada kyautar na urar, Farfesa Mahmoud Daneji, ya ce an yi hakan ne domin tunawa da marigayiya mahaifiyarsa.

Ya kuma yi kira ga wadanda suka ci gajiyar ayyukan da aka gudanar a unguwar, da su yi wa mahaifiyar wanda ya bada gudunmawar addu’a, da shi kansa da kuma dukkan iyalanta.

Slide Up
x