Asirin Wani Gurgun Karya Daya Boye Hodar Iblis Ta N72bn A Jikin Keken Guragu Ta Cika

Alfijr Ta rawaito Jami’an ’yan sanda sun gano wata hodar Iblis da ta kai fam miliyan 1.2 dai dai da Naira biliyan 72 da aka boye a jikin keken guragu a kasar Italiya.

Alfijr Labarai

Wani ɗan leken asirin ’yan sanda ne a filin jirgin saman Malpensa da ke Milan, babban birnin Italiya ya taimaka wa ’yan sandan wajen gano inda aka boye ta.

Mutumin da yake amfani da keken guragun ya nuna kansa a matsayin nakasasshe, kuma ’yan sandan da ke aiki a filin jirgin saman sun gano hodar Iblis din ce cushe a jikin keken.

Nan take ’yan sandan suka kama mutumin, wanda yabiyo jirgin da ya taso daga Jamhuriyar Dominikan, kasar da ake amfani da ita wajen safarar miyagun kwayoyi zuwa kasar Italiya.

Alfijr Labarai

Lokacin da dan leken asirin ya ja hankalin ’yan sandan kan keken guragun, sun duba kayan da mutumin ke dauke da su amma ba su ga komai ba.

Daga nan suka yanke kayan da ke jikin keken guragun, inda a nan ne suka samu hodar Iblis din.

Da mutumin ya ga asirinsa ya tonu sai ya mike tsaye ya fara tafiya, inda mutane da ke wajen suka cika da mamaki.

Alfijr Labarai

An kama fakiti 11 na hodar Iblis mai nauyin kilo 13.25, kuma an kiyasin mutum 27,000 za su iya amfani da ita, kamar yadda ’yan sandan suka bayyana wa manema labarai.

Kimar hodar Iblis din za ta kai Yuro miliyan 1.4.

Amimiya

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *