Jam’iyyar NNPP ta ce ba za ta bari Sanata Rabiu Kwankwaso ya nemi tikitin shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2027 ba.
Sakataren Ƙ jam’iyyar na ƙasa, Ogini Olaposi, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Legas, inda ya ce tikitin 2027 a buɗe yake ga dukkan sahihan mambobin jam’iyyar.
Olaposi ya ce an hana Kwankwaso sake tsayawa takara ne sakamakon sabanin da ya shiga da NNPP da kuma ƙungiyar Kwankwasiya , tare da bayyana cewa yarjejeniyar da aka kulla tsakanin jam’iyyar da ƙungiyar ta ƙare bayan zaɓen 2023.
Ya ƙara da cewa an kori Kwankwaso da wasu jagororin Kwankwasiya saboda ayyukan cin amanar jam’iyya, kuma har yanzu ba a janye hukuncin ba.
Ya ce NNPP tana maraba da masu niyyar tsayawa takara da haɗin gwiwa da sauran jam’iyyun siyasa masu irin akida ɗaya, inda ya jaddada cewa shugabancin NNPP ne kaɗai ke da ikon yanke duk wani hukunci kan haɗin gwiwa a 2027.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t