Matar Da Aka Mancewa Almakashi A Cikinta, Bayan Yi Mata Tiyasa A Asibitin Abubakar Imam Ta Rasu

IMG 20260113 WA0085

Daga Aminu Bala Madobi

Jaridar Alfijir Labarai ta tabbatar da rasuwar wata mata mai suna Aishatu Umar da misalin ƙarfe 1:00 na dare jiya a Kano.

Marigayiyar uwa ce da yara biyar kuma tana da miji. Ta shafe watanni tana fama da rashin lafiya a tsaitsaye tun bayan da aka yi mata tiyata a Asibitin Kula da Cututtukan Mafitsara na Abubakar Imam a watan Satumba da ya gabata.

Bayan tiyatar, ta ci gaba da fama da matsanancin ciwon ciki na tsawon watanni huɗu, inda ake ba ta magungunan rage raɗadi kawai ba tare da gano ainihin matsalar ba.

Daga baya ne bayan gwaje gwaje aka gano cewa an bar almakashi ne a cikinta tun lokacin tiyatar farko. An fara shirin sake yi mata wata tiyata domin ceto rayuwarta, amma abin takaici ta rasu kafin a samu damar yin hakan.

Lamarin ya tayar da hankulan jama’a. Iyalanta na kira ga Gwamnatin Jihar Kano da hukumomin kula da aikin likitanci da su yi cikakken bincike tare da ɗaukar matakin da ya dace domin a tabbatar an yi adalci.

ALLAH ya jikanta da rahama Ameen.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *