Babbar Nasarar Da Sabbin Shugabannin Hukumar Shari’a Ta Kano Suka Fara Samu Kwana 8 Da Shigarsu Office

IMG 20250212 172758

Hukumar Shari’ar Muslunci ta jihar Kano karkashin jagorancin shugabanta Sheikh Malam Abbas Daneji  ta fara da kafar dama.

In da hukumar ta sami nasarar musuluntar da wata baiwar Allah mai suna Salina Bulus wadda ta yiwo takakkiya tun daga garin Jos ta zo wannan hukumar a yau Laraba 12th Feb 2024 Wanda yayi dai-dai ga 13 ga Shaaban 1446 domin karbar kalmar Allah.

Alhamdulillah wannan aiki ya sami jarogarncin Daraktan yaɗa addinin Musulunci na hukumar wato Muhammad Abu Musa, wanda Kwamishina na ɗaya  Sheikh Gwani Hadi da Kwamishina na biyu Malam Ali Dan Abba suka tabbatar da niyyarta, kuma suka bata kalmar addinin musulunci, wanda yanzu haka ta karbi kalma kuma ta zabi sunan Nana A’isha

A’isha ta bayyanawa jaridar Alfijir Labarai cewar zabin ranta ne ya sa taga da cewar shigowa wannan addinin mai tsafta mai tausayi, da jin kai!

Ta kuma bayyana cewar a shirye take kan duk wani kalubale da zai risketa a kan wannan musuluntar da tayi ta amince da shi kuma zata karbe shi.

Alfijir Labarai na taya shugaban hukumar Shari’a ta Kano da kwamishinoninsa da daractocinsa murnar wannan babban aikin Alherin da suka fara a wannan rana, Allah ya yi riko da hannunsu.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *