Shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano, Ambasada Haruna Zago ya rasu bayan fama da rashin lafiya.
Daya daga cikin ma’aikatan hukumar ne ya shaidawa manema labarai rasuwar Dan Zago din.
Ya ce za a yi jana’izar sa a gidan sa da ke Kurna, Tudun Bojuwa, kusa da Kunya Chemist a yau Alhamis da misalin ƙarfe 1 na rana.
Dan Zago dai fitaccen dan siyasa ne a jihar Kano, wanda da shi aka riƙa yakin neman zaben tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
A ranar 5 ga watan Yulin 2023 ne gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nada marigayi Haruna Zago a matsayin Shugaban hukumar kwashe shara ta Kano.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ