Babu Komai Cikin Shirin Raba Kudaden Rage Radadin Tallafin Cire Man Fetur A Gwamnatin Tinubu illa Damfara
Alfijir labarai ta rawaito Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce, dawo da tallafin Man Fetur shi ne mafita yadda talakawan Nijeriya Za su Samu sauki, amma bayar da tallafin kuÉ—i da Gwamnatin tarayya ta ce za ta yi bashi da wani Amfani yaudarace tsantsa.
Ya kara da cewar, a irin wannan mayuyacin yanayi babu wata mafuta da wannan tsari zai kawo, idan har gaskiya ne to ba wannan hanya za abi ba wajen rabon tallafin ba, matukar so ake kowanne talaka ya samu.
ku duba ku ga yanda mafi rinjayen al ummarmu na Arewa maso Yamma suke rayuwa, kaso nawa ne suke amfani da asusun banki? Amsa bayyane take yan kalilan ne, Kaga kai tsaye sai dai mu kira wannan abun yaudara da damfara kawai ga al ummarmu.
Kwankwaso yace: Bari na baka wani misali amatsayina na wanda ya rike chairman na harkokin banki na shekara hudu. na san al amura irin wannan da suka shafi kudi da tattalin arziki,.
Al ummar Arewa Kashi saba in zuwa da biyar 70/75 duk basu da wani Abu Account, ka isa kace wayan nan mutane da suke kada mafi rinjayen kuria a zabe basu da Amfani?
Ya zama wajibi mu wakilan Arewa mu farka domin idan bamu yunkura ba, Za a ci da rabon al ummarmu, kuma sai Allah ya kamamu.
News NG
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V