Badakala! EFCC Sun Kama Shugaban Hukumar Makamashi Kan zargin kwashe Naira Biliyan 500

FB IMG 1778747984611

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta kama Darakta-Janar na Hukumar Makamashi ta Najeriya (ECN), Mustapha Abdullahi, bisa zargin almundahanar kuɗi.

Wata majiya daga hukumar ta EFCC ta ce an kama shi ne a Abuja, kuma a halin yanzu yana hannun hukumar domin ci gaba da bincike.

Majiyar ta bayyana cewa, kuɗaɗen da ake zarginsa da su sun kai kusan Naira biliyan 500.

Har yanzu EFCC ba ta fitar da cikakken bayani a hukumance ba, kuma ƙoƙarin jin ta bakin kakakinta bai yi nasara ba.

An naɗa Mustapha Abdullahi a matsayin shugaban hukumar makamashi ta ƙasa a watan Oktoba 2023, bayan ya shafe fiye fa shekaru 10 yana aiki a Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur NUPRC.


Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *