Daga Aminu Bala Madobi
Rahotanni masu ƙarfi da Jaridar Alfijir Labarai ta samu sun rawaito cewar korar tsohon Ministan Kuɗi, Wale Edun, ba ta rasa nasaba da matsalar rashin jituwa da Shugaba Bola Tinubu.
Wasu bayanan karkashin kasa sunce dangantaka ce tayi tsami matuka tsakanin mutanen biyu a ‘yan watannin nan, lamarin da ya haifar da rashin amincewa da yadda ake tafiyar da harkokin kuɗin gwamnati.
Majiyoyin sun ce shugaban ƙasar ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda aka tsara kasafin kuɗi, musamman dangane da rashin ware isassun kuɗaɗe domin manyan ayyukan raya ƙasa. Ana zargin cewa ma’aikatar kuɗi ƙarƙashin jagorancin Edun ta fi mayar da hankali kan kashe kuɗaɗen yau da kullum maimakon saka jari a muhimman ayyukan ci gaba da al’umma za su amfana da su.
Wannan rashin jituwa ya haifar da zazzafar muhawara a tsakanin manyan jami’an gwamnati, inda wasu ke ganin cewa rashin aiwatar da muhimman ayyukan raya ƙasa na iya jefa gwamnatin cikin suka daga jama’a. Hakan ya sa shugaba Tinubu ya ɗauki matakin sauya akalar ma’aikatar kuɗi domin tabbatar da cewa an bai wa ayyukan ci gaba fifiko a tsarin kasafin kuɗin ƙasa.
Ko da yake har yanzu ba a fitar da wata sanarwa a hukumance da ke bayyana cikakken dalilin korar tasa ba, bayanan da ke fitowa daga ciki na nuna cewa wannan mataki na da alaƙa kai tsaye da sabanin fahimta tsakanin ministan da shugaban ƙasa. Ana sa ran cikin kwanaki masu zuwa gwamnati za ta bayyana cikakken matsayinta kan wannan lamari da ya girgiza fagen siyasar ƙasar.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t