Bankin CBN Ya Buƙaci Ɗalibai Su Riƙa Biyan Kudin Makaranta Da e-Naira

Alfijr ta rawaito Babban bankin Nijeriya CBN ya shawarci ɗalibai da su yi amfani da tsarin Naira ta yanar gizo, wacce aka fi sani da e-Naira wajen biyan kudin makaranta da sauran kuɗaɗe a ƙasar.

Shawarar ta zo ne a yayin wani taron wayar da kai a kan amfani da e-Naira a Jami’ar garin Lagos a Akoka.

Rakiya Muhammad wadda take Darakta, Sashen Fasahar Watsa Labarai na Babban Bankin CBN kuma Kodineta, Kwamitin Ayyuka na Fasaha, ta bayyana cewar taron wani ɓangare ne na ƙoƙarin da babban bankin kasar ke yi na ganin cewa babu wata kungiya ta ƴan Nijeriya da aka hana su damar amfani da kuɗin yanar gizo.

Daraktan, wacce jami’i a ce a Sashen Fasahar Sadarwa na Babban Bankin, Khalipha Nuhu ya wakilta a wajen taron, ta ce: “Mun dade mu na hada hannu da kungiyoyi da cibiyoyi da dalibai da dama a wani bangare na hadafin da muke yi shi ne kowa ya zama yana cikin tsarin a ƙasar.

Ta tace dalibai sune makasudin haɗin gwiwarmu da kuma inda mafi kyawun shigar da ɗalibai fiye da a jami’a.

Don haka ne ma ya sa muka zo a yau domin tattaunawa da dalibai da al’ummar Jami’ar domin wayar da kan su san menene eNaira da kuma dora su kan manhajar

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Slide Up
x

One Reply to “Bankin CBN Ya Buƙaci Ɗalibai Su Riƙa Biyan Kudin Makaranta Da e-Naira”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *