Alfijr ta rawaito wata kotun magistrate da ke zamanta IKeja da ke birnin Ikko ta tsare wata mata mai suna Folake Adeleye mai shekaru 34 a bisa zarginta da lakadawa wani dan sanda dukanbkawo wuka a yau Alhamis.
Alfijr Labarai
Wacce ake karar, yar kasuwa ce da ke zaune a Agege Lagos, ana tuhumarta da laifin kai hari da dukan tsiya ga jami in tsaro
Lauyan mai shigar da kara, Insp Funmilayo Akinleye, ya shaida wa kotun cewa wanda ake karar, ta ladawa dan sanda Ridwan Lasaki, ya sha duka a lokacin da yake gudanar da aikinsa na doka.
Akinleye ya ce mijin wanda ake zargin ya kai karar matarsa, inda ya zarge ta da rikicin cikin gida.
Alfijr Labarai
Mai gabatar da kara ya kuma ce an aika mai karar ne ya kama ta. “Da isa gidan, wanda ake kara, ta ki amincewa da kamatan, kuma ta lakada wa dan sandan duka har da cizon hannunsa,” in ji ta.
Laifin, da kara, ya ci karo da tanadin sashe na 174 na dokokin manyan laifuka na jihar Lagos, na shekarar 2015.
Sai dai wanda ake tuhuma, ya musanta aikata laifin.
Alfijr Labarai
Alkalin kotun, Misis O. O Fajana ta bayar da belin wanda ake kara a kan kudi N20,000 tare da mutane biyu da za su tsaya mata
Fajana ta dage sauraron karar har zuwa ranar 28 ga watan Satumba.