Bola Tinubu Ya Gwangwaje Ƴan Kannywood kyautar Miliyan 50

Alfijr ta rawaito Ɗan takarar shugaban ƙasa a APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bai wa masana antar Kannywood kyautar naira miliyan 50 a matsayin gudunmawar sa ga cigaban masana’antar.

Alfijr Labarai

Asiwaju ya ba da kuɗin ne a lokacin da ya halarci wani taro na musamman da ‘yan fim su ka shirya masa a daren ranar Lahadi a fadar Gwamnatin Jihar Kano.

Da ya ke jawabin manufar shirya taron, furodusa Abdul Amart Maikwashewa, ya ce: “Wannan taro na matasa ‘yan fim ne masu goyon bayan tafiyar Tinubu su ka shirya a ƙarƙashin Gidauniyar Kannywood domin su nuna irin ƙarfin goyon bayan da ya ke da shi a cikin ‘yan fim.

Dakta Ahmad Sarari wanda Shi ne shugaban ƙungiyar masu shirya Fina finai ta Nijeriya (MOPPAN) na ƙasa, ya bayyana Kannywood da wata babbar masana’antar da ta ke kawo kuɗin shiga da kuma samar da aikin yi ga matasa, don haka ya yi kira ga Tinubu da ya duba yadda masana’antar ta ke idan an kai ga nasara.

Alfijr Labarai

A nasa jawabin, jarumi kuma tsohon shugaban MOPPAN, Alhaji Sani Mu’azu, ya yi kira ga ɗan takarar da ya zuba ‘yan fim a cikin yaƙin neman zaɓen sa saboda karɓuwar su ga jama’a da kuma masoya masu yawa da su ke da su.

Shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu na ƙasa, Gwamna Samuel Lalong na Jihar Filato, lokacin da ya ke mayar da martani, ya tabbatar wa da ‘yan fim ɗin cewa tuni su na cikin kwamitin, kuma za a Ƙara saka wasu. 

Haka kuma ya tabbatar da gudunmawar naira miliyan 50 ga Kannywood da Tinubu ya ba su domin inganta masana’antar.

Alfijr Labarai

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *