BUƊADDIYAR WASIƘA GA MASU GIDAJEN REDIYO, JAGORORI, DA ’YAN JARIDA A KANO

IMG 20260208 WA0841

Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu
Wannan wasiƙa ba ta zuwa da zagi, ba ta zuwa da tayar da hankali, kuma ba ta zuwa da nufin nuna yatsa ga wani kai tsaye.

Ta zo ne domin tunanarwa, gyara, da tambayar kai tsaye,

Ina gizo ke saka?

A cikin makonin nan, sama da ’yan jarida biyar sun ajiye aikinsu daga mabanbantan gidajen rediyo a Kano.

Daga Ammasco Radio, akwai Hidaya Salisu Ahmad, mataimakiya a sashen labarai, da Halimatu Abdullahi, shugabar sashen labaran.

Daga Hikima Radio, Aliyu Sufya daga sashen siyasa, da Abubakar Isa Dandago, Janar Manaja.

Sai kuma daga Dala FM, Abba Haruna Idris, daga sashen siyasa kuma DCA.

Waɗannan sunaye ba ƙananan ma’aikata ba ne, Mutane ne da suka shafe lokaci, suka ba da ƙarfi, suka ba da tunani wajen bada gudummawa a tashoshin.

Tambayata ga kowa da kowa ita ce: Wa aka taba ji gidan rediyonsa ya fito fili ya ce “mun kori wane”?

Wa kuma ya bar aik bai fito fili ba yace  “dan radin kansa ya bari ba?

Me ya sa kusan duk waɗanda ke barin aiki ba sa faɗin takamaiman dalili?

Me ya sa ake sauƙaƙa magana a ce albashi ne kawai?

Me ya sa ba a yawan jin labarin *cusgunawa*, *tsangwama*, da *wulakanci* daga wasu jagorori, ba daga mamallaka kafar ba?

Me ya sa kullum kai ake gani, kai ake wa alfarma ba tsarin adalci ga kowa ba?

Waɗannan tambayoyi ba don lalata suna aka yi su ba, an yi sune domin a duba madubi.

*Ga ’yan jarida kuwa,* wannan sako ne kai tsaye:
Malamdan jarida, abu na farko
ka san kanka ba girman kai ba, ba tumasanci ba.

Ka gane cewa kai ne a gaba-gaba, kai ne kake mu’amala da damuwar mutane, kai ne kuma kake cikin haɗari fiye da kowa.

Ka tsare mutuncinka.
Kada tsoron a kore ka ya sa a dinga cin mutuncinka babu gaira babu dalili, aiki kake yi ba bautar wani ba.

Tsakaninka da shugabanni,
shawara da girmamawa ne, ba hayaniya ba, ba cin mutunci ba.

Ka tsaya kan aikinka da rikon amana, Ka guji munafunci, gulma, da side talk a tsakaninku.

A hasashena na kaina, kuma ina faɗin wannan da cikkaken alhaki ba mamallakan gidajen rediyo ne kai tsaye ke tilasta wa ma’aikata barin aiki ba.

A mafi yawan lokuta, abubuwan dake faruwa a ciki gilli ne, tsangwama, tsana mara dalili, da amfani da iko ba bisa ka’ida ba, sune ke gurgunta zuciya har ta gaji.

Wannan ba zato ba ne, wani abu ne da ya faru da ni da kaina, Kuma idan lokaci ya yi, sunaye za su fito.

A karshe, wannan kira ne na girmamawa ga masu gidajen rediyo: Ku buɗe kofar sauraron korafe-korafen ma’aikata.

Ko ta hanyar akwatin sirri da kowa zai iya rubuta damuwarsa ya jefa a ciki, ko zama na wata-wata da jagorori da mamallaka kafar za su karanta su tare, ba don hukunci ba, amma don fahimta.

Ba don tsoro ba, amma don gyara, Domin rediyo ba kango ba ne mutane ne, dan Idan mutum ya gaji a ciki, sauti zai mutu a waje.

Wannan wasiƙa a buɗe take
ga kowa da kowa.

(C) ALIYU WALI
  CHIROMAN MUHASA

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *