Budaddiyar Wasika Ga Prof Shehu Abdullahi Maaji Shugaban Hukumar Northwest Development Commission

IMG 20250415 100650

Assalamu Alaikum

Yayana Professor Shehu Abdullahi Maaji ina taya ka murna da Allah ya baka wannan matsayi mai girma na shugaban hukumar cigaban arewa maso yamma.

A ganina wannan matsayi dai-dai yake da matsayin da Ahmadu Bello sardaunan sokoto ya riƙe a jamhuriyar ta farko. Watakila ma yafi nasa domin yawan jama’ar dake ƙarƙashin ka yanzu yafi na wancan lokaci.

A matsayinmu na kannenka wannan abin alfahari ne a wajen mu, kuma abin mu tausaya maka ne. Zamuyi alfahari da kaine domin wannan matsayin ya nuna mana cewa hanyar da kake kai wacce kuma ka dora mu akai ta riko da addini hanya ce mai jawowa mutum daukaka duniya da lahira. Don haka ba zamuyi nadama akan binka ba. Zamu tausaya maka ne kuma domin wannan matsayin yazo maka a lokaci mai wuya wanda zai sa ka fuskanci kalubale mai yawa musamman ma daga marasa kishin arewa. Amma ina rokon Allah ya buda kirjinka, Ya haskaka gabanka da bayanka kuma yayi maka katangar karfe da irin wadannan mutane.

Yayana ina da shawarwari a gare ka.

Na farko dai arewa maso yamma tana cikin wani hali na rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali. Rashin tsaro yakai har Sarkin yanka aka kama aka kashe a cikin kasarsa. Ina baka shawara ka samar da wata runduna mai karfi wacce zata kunshi dukkan jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki daga dukkan jihohin nan bakwai ta yadda zasu yi aiki don kawo karshen wannan matsala.

Na biyu ina baka shawara ka ɓullo da wani shiri mai girma na aikin noma wanda zai bada dama jihohin mu su rika aiki tare da manufa iri daya domin samar da abinci. Ka tuna cewa Ahmadu Bello sardaunan sokoto ya shirya ciyar da Africa da shinkafa daga noman Kano da Sokoto kaɗai. Wannan dajin da yan ta’adda suke buya cikinsa arziki ne amma bama amfani dashi shi yasa suke buya cikinsa.

Na uku, ka samar da bangare a ma’aikatar nan wanda zai kula da ma’adanai da albarkatun karkashin kasa da muke dashi domin amfanin jama’ar mu. Ina so in tunatar da kai cewa muna da ma’adanai da zasu iya rike mu ba tare da man fetur

Na hudu, ka samar da hanyoyin sufuri wadanda zasu hada mutanenmu. Abun mamaki yanzu idan kana son jirgin Sokoto daga Kano sai kayi biye biye. Me zai hana mu samar da hanyoyin jirgin kasa daga ko’ina cikin jihohin mu ta yadda mutum zai iya tashi daga Katsina yaje Kebbi ko zamfara ko Kano ko Jigawa duk a jirgin kasa. Wannan ba karamin cigaba zai kawo mana ba. Sannan ya samar da ayyukan yi da rage hadarin mota da kullum yake kashe mutanen mu.

Na biyar, ka kawo sauyi a harkar ilimi. Manhajar karatun da ake koyarwa yanzu ta tsufa bata dace da zamani ba. Me zai hana ku samarwa makarantun mu manhajar zamani wacce ta dace da addini da al’adunmu. Lokaci yayi fa da za’a fara koyar da ilimi cikin harshen Hausa. Yanzu dai ga kasar Nijar ta dauki Hausa a matsayin harshen gwamnati. Wannan fa manuniya ce cewar zamani yazo da kowa zai koma gidan ubansa. Dama Malam Aminu Kano yace “Nigeria ɗaya ce Amma kowa ya san gidan ubansa” Muje zuwa babban yaya.

Na shida, ina baka shawara ka yi taka tsantsan da yan tayi daɗi wadanda basu san komai ba sai a basu kwangila, su ki yin kwangilar su cinye kudin kuma suje wajen manya suce a basu kariya. Na san ka a matsayin malami mai addini da taka tsantsan da duniya. Bana zaton za’a hada baki da kai wajen lalata arewa.

A Karshe ina maka fatan alheri. Ina rokon Allah ya tsare ka, Ya baka iko da koshin lafiya da tsawon rai da jama’a zasu ga irin baiwar da Allah yayi maka.

Nine kaninka

Barr Muhammad Sani Yunusa ©®

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *