Daga Aminu Bala Madobi
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Fatakwal ta yanke hukunci kan gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, inda ta bayar da umarnin tsige Gwamnan Rikon Kwarya da shugaba Bola Tinubu ya nada.
Hukuncin kotun, wanda aka yanke a ranar Talata, ya baiwa wanda Tinubu ke goyon bayansa wa’adin sa’o’i 48 ya fice daga harabar gidan Gwamnati, inda ya kara tabbatar da wa’adin mulkin Gwamna Fubara a matsayin zababben Gwamnan jihar Ribas.
Mai shari’a Boma Diepriye, wanda ya jagoranci shari’ar, ya yanke hukuncin cewa nadin da shugaban kasa ga Wanda zai kula da al’amuran jihar maimakon zababben gwamna da aka zaba bisa tafarkin dimokuradiyya “ba abune karbabbe ba, kuma hakan ya saba ka’ida.”
Kotun ta jaddada cewa kundin tsarin mulkin Najeriya bai bayar da damar yin irin wannan nadi ba a cikin sashin Dokokin na kotunan tarayya inda ba a tsige gwamna ba kuma ba a yi masa adalci ba.
Yanzu haka ana dakon martanin Bangaren Gwamnan Rikon Kwarya dakuma fadar Shugaban kasa kan wannan Kwarya kwaryan hukunci.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD