Burina Shine Kare Martabar Jihar Kano Duba Da Yadda Ake Mata Fyade- Muhyi Magaji

Alfijr ta rawaito tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano Muhyi Magaji Rimin Gado ya ce ba wai NNPP ke kadai ke zawarcina ba har da Jam iyyar ADP

Alfijr Labarai

Muhyi a yayin tattaunawarsa da wakilin Alfijr, ya jaddada cewar a tsarin siyasar sa baya yin ta don buƙatar kai ko yayi anti fati, kawai yana siyasa ne don kishin jihar Kano da cigabanta

Ya kuma bayyana cewa, gaskiya ne muna maganganu da jam iyya mai kayan marmari wato NNPP domin magana muke ta jihar Kano ba magana akan Muhyi ba ko Makomarsa ba.

Idan kuka kalla za ku ga cewar abubuwan da suke faruwa a jihar Kano ko kare ba zai ci ba, kotuna basu tsira ba makarantu da Asibitin duk sun shiga halin ha ula i, kun ga ya zama dole muyi kokarin hada karfi da karfe domin ceton jihar. In Ji Muhyi

Alfijr Labarai

Magaji ya kara da cewa ni yanzu burina shine kare mutunci Kano duba da yadda ake yiwa jahar Fyade kamar yadda ake yiwa mata haka ake yiwa Kano, kuma tsarin shugabanci ba haka ya ke ba duba da yawanci gani suke sun sami dama dole a sha romo gara ta faɗi ayi komai ba komai

Tabbas gaskiya ne wasu masu fada aji ƴan jam iyyar P D P suna yi wa jam iyya mai mulki aiki! Tun ana gayamin bana yadda har sai da na kallon kurilla na gano ne, don haka na yadda mu zo mu haɗa kai don mu fidda Ai daga rogo.

Muhyi ya kara da cewar duk wani shugaba da yake yiwa al umma wani nau in zalinci, to tabbas lokaci yayi da jama a za su karkade kuri unsu su yaki ko wanene, domin yin hakan shi zai nunar da na baya jama a sun farka.

Alfijr Labarai

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Slide Up
x

One Reply to “Burina Shine Kare Martabar Jihar Kano Duba Da Yadda Ake Mata Fyade- Muhyi Magaji”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *