DA Ɗumi Ɗumins Babban bankin Najeriya Ya Fitar Da Fasalin Sake Takardun Kudi Na N200, N500 Da N1,000

Alfijr ta rawaito babban bankin Najeriya CBN ya ce zai sake fasalin kudin N200, N500 da N1,000 bi da bi.

Alfijr Labarai

Gwamnan babban bankin na CBN, Godwin Emefiele ne ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai na musamman a Abuja, a ranar Laraba, 26 ga watan Oktoba, 2022.

Ya ce an dauki matakin ne domin ganin an shawo kan kudaden da ke yawo.

A cewarsa, mafi yawan kudaden da kasar nan ke da su, a wajen bankuna ne, kuma CBN ba za ta bari lamarin ya ci gaba ba.

Ya kara da cewa daga ranar 31 ga Janairu, 2023, tsofaffin takardun ba za su daina zama takardar doka ba

Alfijr Labarai

Daga yanzu, za a dakatar da cajin bankunan da ake yi wa ajiya domin ana mayar da tsofaffin takardun naira zuwa bankuna.

Ya tabbatar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da izinin sake fasalin, samarwa, da rarrabawa

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

2 Replies to “DA Ɗumi Ɗumins Babban bankin Najeriya Ya Fitar Da Fasalin Sake Takardun Kudi Na N200, N500 Da N1,000

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *