Da Ɗumi Ɗuminsa! An Nada Tsohon Shugaban Riko Na Jami’ar MAAUN Mukamin Babban Sakataren Kungiyar AAPU

Alfijr ta rawaito shugaban Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) kuma Shugaban Kungiyar Jami’o’i Masu Zaman Kansu na Afrika (AAPU) ya nada tsohon shugaban riko na Jami’ar MAAUN dake Kano, Farfesa Mohammad Sanusi Magaji Rano a matsayin sabon Sakatare Janar na kungiyar AAPU.

Da yake gabatar da takardar nadin ga Farfesa Rano a ranar Talata a wajen wani biki da ya gudana a Jami’ar, wanda ya kafa jami’ar, ya ce ya yi nadin ne saboda gudunmuwar da Farfesa Rano ya bayar wajen ganin an samu nasarar Jami’ar MAAUN Kano ta fara aiki.

Farfesa Gwarzo, ya yaba wa tsohon shugaban riko bisa sadaukarwar da ya yi, ya ce ya dauki matakin karrama Farfesa Rano ne bisa jajircewa da kuma son ganin wanda aka nada ya kawo basirarsa kan sabon aikin da aka ba shi.

Alfijr

Lokacin da muke neman lasisi daga hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa, Farfesa Rano ne ya yi wannan gwagwarmayar.

Abu ne mai muhimmanci cewa mun sanya shi a matsayin shugaban kula da Sashen digiri na biyu da na uku a Maradi, daga baya kuma aka nada shi a matsayin shugaban riko na MAAUN Kano.

Alfijr

Farfesa Gwarzo ya kara da cewa don haka muna son ka kara kaimi fiye da yadda muka saka a baya, bisa wannan sabon nadin.

Sannan yayi amfani da wannan dama wajen yabawa ma’aikatan MAAUN ta Maradi bisa yadda suka samar da nagartattun dalibai wanda hakan ya karfafawa sauran dalibai masu neman gurbin shiga Jami’ar MAAUN Kano, babban aikin da muka yi a Maradi shiyasa muke da dalibai da dama da ke son zuwa MAAUN Kano domin yin karatu.

Alfijr

Farfesa ya kara da cewar, Nijar ita ce asalinmu, a nan ne na tattara dukkanin ilimin da yasa na zo na kafa MAAUN Kano, daga cikin jami’o’i masu zaman kansu guda 25 da aka bai wa lasisi a lokaci guda da MAAUN, babu daya daga cikinsu da yake da daya bisa hudu na abin da muka samu a nan a yanzu.

A cewarsa, sama da dalibai 500 ne aka dauka tare da yi musu rijista a Jami’ar kuma nan da kwanaki masu zuwa za su fara karatu a Jami’ar.

Alfijr

Wanda ya assasa Jami’ar ya jaddada kudirinsa da kuma shirye-shiryensa na samar da isassun kayan aiki da nufin ganin MAAUN Kano ta kasance daya daga cikin mafi nagartan jami’o’i a Nijeriya.

Ya bayyana cewa shirinsa na samar da babbar harabar Jami’ar a Gwarzo nan da shekaru biyu masu zuwa domin bai wa al’ummar da ya fito damar samun ilimi mai zurfi.

Alfijr

A nasa jawabin, Babban Sakataren kungiyar ta AAPU, ya godewa Farfesa Gwarzo bisa wannan karramawar da aka yi masa, ya kuma yi alkawarin yin bakin kokarinsa wajen inganta manufofin kungiyar.

Ya ce kungiyar ta AAPU za ta yi hulda da sauran Jami’o’in kasar Mexico da nufin daukar binciken da jami’o’in Afirka ke yi zuwa kasuwa.

Alfijr

“Mafi yawan jami’o’in gwamnati musamman a Nijeriya ba za su iya yin alfahari da duk wani abu da zai amfanar da al’ummarsu ba, a don haka zan yi hulda da jami’o’in da ke Mexico saboda yawancin binciken da suke yi ana kai kasuwa ne,” in ji shi.

Shima a nasa takaitaccen jawabin, shugaban Jami’ar, Farfesa Mohammad Israr ya taya Farfesa Rano murnar sabon nadin da aka yi masa, ya kuma yi alkawarin tabbatar da ganin ya dorar da nagarta da tsarin MAAUN Maradi a MAAUN Kano domin samar da dalibai masu nagarta da za su yi gogayya da takwarorinsu a fadin duniya.

Slide Up
x