Alh Muhammad Abacha Ya Zama Dan Takarar Gwamna A Jam iyyar P D P A Kano

Alfijr

Alfijr ta rawaito Alh Muhammad Abacha, ya samu nasarar lashe zaɓen Fidda gwani na gwamna a jam’iyyar PDP Kano.

Barista Amina Garba, wadda ita ce ta jagoranci zaɓen, ta bayyana Alh Muhd Abacha a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ƙuri’u 736 inda ya kayar da abokin takararsa Jafar Sani Bello da kuri’u 710.

Shugaban kwamitin zaben,

Muhd Jamu, shugaban kwamitin zaɓen, ya ce an gudanar da zaɓukan nasu ne bisa ka’ida tare da wakilai da hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta turo da hadin guiwar ƴan sanda da jami’an tsaro na jihar.

Slide Up
x