Da Ɗumi Ɗuminsa! Jam’iar Ta Sanar Da Ranar Komawa Karatu A Makarantar

Alfijr ta rawaito Bayero University da ke Kano ta sanar da ranar da za’a cigaba da ayyukan ilimi a Jami’ar

Alfijr Labarai

Bayero, Kano ta sanar da ranar 24 ga Oktoba, 2022 a matsayin ranar da za a ci gaba da ayyukan ilimi, biyo bayan dogon yajin aikin da aka yi a faɗin Kasar.

Sanarwar ta biyo bayan dakatar da yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta yi na tsawon watanni 8.

Wata sanarwa da BUK ta fitar, mataimakin magatakardar hulda da jama’a, Lamara Garba, ya ce hukumar gudanarwar jami’ar bayan taron ta da aka gudanar a ranar Alhamis, 13 ga watan Oktoba, 2022 ta amince da ranar ci gaba da aiki.

Alfijr Labarai

“Saboda haka, ɗalibai za su ci gaba da ayyukan ilimi daga ranar Litinin, Oktoba, 24th, 2022,” in ji sanarwar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *