DA ƊUMI-ƊUMINSA: Sarkin Kano Aminu Ado Bayero Angwance

Alfijr ta rawaito da safiyar wannan rana ta Juma’a 6 ga watan 1 na shekara ta 2023 aka ɗaura Auren Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da Amaryarsa Hauwa’u Adamu Abdullahi Dikko.

An Daura Auren ne a gidan marigayi Jarman Kano Farfesa Isah Hashim dake unguwar Nassarawa a birnin Kano.

Madakin Kano Alhaji Yusuf Nabahani Cigari shine ya kasance wakilin Mai Martaba Sarkin Kano, yayin da Alhaji Shehu Hashim ya kasance a matsayin waliyyin Amarya.

Amaryar wadda ake kira da Hajiyayye, an riga da anyi mata baiko da Mai Martaba Sarkin na Kano ne tun cikin shekarar da ta gabata, wanda ya kasance aka Daura Auren da safiyar wannan rana, kuma ta kasance guda daga cikin zuri’ar marigayi Malam Jamo dan’uwan marigayi Sarkin Kano na 2 a daular Sarakunan Fulani Malam Ibrahim Dabo.

Mahalarta taron Daurin Auren sun hada da Makaman Bichi Alhaji Isyaku Umar tofa da Sarkin Dawaki Mai Tuta na Kano Alhaji Bello Abubakar Tuta da Dan Ruwatan Ringim da sauran mahalarta da dama.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/F86a4baiSZU4aMOt7yuBfE

Slide Up
x

2 Replies to “DA ƊUMI-ƊUMINSA: Sarkin Kano Aminu Ado Bayero Angwance

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *