Da Ɗumi Ɗuminsa! Wata Babbar Jami’a Ta Karrama Idris Ado (Adebo) Da Lambar Dakta

Alfijr ta rawaito Jami’ar ESGT Da ke Ƙasar Benin ta gwangwaje dan gwagwarmaya nan Camarade Idris Ado (Adebo) da karramawar Dacta.

Alfijr Labarai

Idris Adebo na daya daga cikin jami an lafiya masu kula da lafiyar hakora a jihar Kano wato (Dental Therapist)

Dr Adebo ma aikacine a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano AKTH, kuma yana da Asibitin kansa mai suna (Millennium Dental Clinic) sannan kuma shine shugaban Kano State Oral Health Team, wanda ke gudanar da ayyukan Haƙori kyauta a fadin jihar.

A nasu bangaren Shugaban Jami’ar, tare da mukarraban Jami ar sun yanke shawarar ba shi wannan lambar yabo ta girmamawa ne bisa jajircewa da cancantarsa.

Lambar yabon ta fadin Afirka da sauran kasashen duniya ce. In sanarwar.

Alfijr Labarai

ESGT UNIVERSITY BENIN tana cikin manyan Jami’o’i 10 a Jamhuriyar Benin kuma Ma’aikatar Ilimi da Bincike ta Kimiyya ta Jamhuriyar Benin ta amince da ita, haka kuma ma’aikatar Ilimi ta tarayya, Najeriya ta amince da shi a ranar 11 ga Oktoba, 2022

Jami’ar ta ba da wannan lambar yabo ga mutanen da ke da kyawawan halaye don gudummawar da suke bayarwa ga bil’adama a fannonin ilimi, siyasa, ƙarfafa tattalin arziki, kula da zamantakewa, tunani, da sassan ci gaba.

Alfijr Labarai

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Slide Up
x

2 Replies to “Da Ɗumi Ɗuminsa! Wata Babbar Jami’a Ta Karrama Idris Ado (Adebo) Da Lambar Dakta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *