Dan Kano ya Zama Shugaban Kungiyar Injiniyoyi ta Duniya (World Federation of Engineers).

Alfijr

Alfijr ta rawaito Injiniya Mustafa Balarabe Shehu Bakano na farko ya zama Shugaban Kungiyar Injiniyoyi ta Duniya (World Federation of Engineers).

An zabe shi a matsayin Shugaban Kungiyar Injiniya ta Duniya, WFEO. Wannan ba karamin aiki ba ne da dan Najeriya da dan Afirka suka samu.


Injiniya Mustafa Balarabe Shehu daga dama wato sabon shugaban kungiyar, sai Farfesa Jose Vieira a tsakiya da kuma Injiniya Tasiu Wudil sanye da babbar riga

Alfijr

Engr. M. B. Shehu, FNSE, FAEng shine tsohon shugaban kungiyar Injiniyoyi ta Najeriya (NSE), Engr. Mustafa Balarabe Shehu, FNSE, FAEng. an maido da shi a matsayin zababben shugaban kungiyar Injiniya ta Duniya (WFEO) a zaben da aka gudanar a babban taron koli na kungiyar Injiniya ta duniya a San Jose, Costa Rica.

Engr. Shehu ya samu kuri’u 67 daga cikin kuri’u 71 da ya samu nasara a zaben.

Yana da kyau a lura cewa Engr. Shehu shi ne bakar fata na farko da ya ci zabe a matsayin babban jami’i mafi girma a kungiyar Injiniya a fadin duniya.

Idan dai za a iya tunawa Engr. Mustafa Shehu ya kasance Mataimakin Shugaban Hukumar WFEO bayan ya lashe zabe a taron Injiniya na Duniya da aka yi a Australia a 2019.

Alfijr

Yanzu haka shi ne zai karbi ragamar shugabancin WFEO a Prague, Jamhuriyar Czech a watan Oktoba 2023, a lokacin babban taron kungiyar Wannan zaben shi ne, nasara ga kungiyar Injiniya ta Najeriya, nasara ga Najeriya da nasara ga Afirka.

Ina taya daukacin membobin NSE murna. Sa hannun Abdulkadir Aliyu Ag. Babban Sakatare

Slide Up
x