Da Ɗumi-Ɗuminsa: Gwamnatin Nijeriya Ta Haramta Amfani da “Dr” Ga Masu Digirin Girmamawa

IMG 20260506 WA0224

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sanar da haramta amfani da lakabin “Dr” ga sunayen mutanen da aka bai wa digirin girmamawa (Honorary Degree), inda ta ce daga yanzu ba za a amince da amfani da wannan lakabi ba sai ga wadanda suka kammala karatun digirin digirgir ta hanyar bin ka’idojin ilimi na jami’a.

Wannan mataki na zuwa ne domin kare martabar ilimi da kuma dakile yadda ake amfani da lakabin ba tare da cancantar da ta dace ba.

Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta bayyana cewa digirin girmamawa ana bayar da shi ne domin karramawa da yabawa ga gudunmawar da mutum ya bayar a al’umma, ba wai domin ya zama hujjar amfani da lakabin “Dr” a gaban suna ba.

Hukumar ta ce yawaitar amfani da lakabin daga masu irin wannan digiri na haifar da rudani tare da rage kima da mutuncin masu digirin digirgir na hakika da suka shafe shekaru wajen gudanar da bincike da karatu.

Masana ilimi da dama sun yi maraba da wannan mataki, suna mai cewa zai taimaka wajen dawo da darajar ilimi da gaskiya a cikin al’umma. Sun kuma bukaci jami’o’i da cibiyoyin ilimi su kara fayyace wa wadanda suke karramawa iyakar amfani da takardar digirin girmamawa domin kauce wa rikice-rikice da yaudara a tsakanin jama’a.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *